Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kenye West Ya Kai Ziyarar Bazata Kasar Haiti


Shugaban Kasar Haiti Jovenel Moise, tare da Kenye West.

Mawakin Gambara kuma dan takarar shugaban kasar Amurka na uku Kenye West, ya kai ziyarar bazata kasar Haiti, shugaban kasar Haiti Jovenel Moise ya sanar ta shafin Twitter.

“Ina tare da fitattcen mawakin Gambarar Amurka Kenye West, wanda yanzu ya kawo mana ziyara. Ina masa fatan jin dadin ziyarar.” Shugaba Moise ya kafe a shafin Twitter.

Wannan sanarwa wadda ta hada da hotuna hudu, sun nuna shugaban kasa Moise da Kenye West sanye da takunkumi a fuskokinsu.

Ba a san dalilin wannan ziyara da Kenya ya kai kasar dake yankin Karabiyan. Sai dai shi bai kafe komai ba a shafinsa Twitter @kanyewest ba.

Kamar yadda kafofin labaran yankin suka bayyana, shahararren mawakin ya sauka kasar Haiti ne ranar Juma’a da safe, ya kuma hadu da shagaban kasar wanda ya zagaya da shi wasu kyawawan tsibiri biyu da ke yawan zuwa yawon bude ido.

Kenye West ya sanar da tsayawarsa takarar shugaban kasar Amurka ranar 4 ga watan Yuli na 2020, a hukumance kuma zai fito a takardun kuri’un zaben watan Nuwamba a jihohin Amurka 11.

Facebook Forum

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG