Koch na kungiyar kwallon kafar Liverpool yace yana bukatar ‘yan wasan shi su kafa wani sabon tarihi a kungiyar.
Mr. Brendan Rodgers ya kalubalanci ‘yan wasan shi da kowanne ya yi rawar gani da duniya bazata manta da shiba a kungiyar ta Liverpooll a wasan da zasu buga ranar Talata.
Nasara da kawai kungiyar take nema a rukunin B na wasan cikin gida da za’a gwabza da kungiyar Basel wannan ka dai ya ishi kungiyar tasamu dama don shiga gasar wasannin zakaru na UEFA.
Ita kuwa kungiyar kwallon kafar Anfield tasamu damar lashe babbar kyauta ta kungiyar kwallon kafar kasashen turai a karo na 5 a shekar 2005.
-
Yusuf Harande
Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.