WASHINGTON, DC —
Koch na kungiyar kwallon kafar Real Madrid Carlo Ancelotti, yace yana da tabbacin kungiyar tashi zata cigaba da jarumtaka, wanda kokarinsu na iya kaisu kowane mataki.
Kungiyar ta samu nasar lashe wasanni gomasha bakwai 17 a wasannin zakaru na kasashen turai, wanda shiyasa tazama ta sama bayan wasanni gomasha uku 13 na laliga.
Kungiyar da ta samu damar zama ta farko a rukunin wasa camfiyons lig. Bayan samu kololuwar maki a wasanninsu fiyar 5, kuma Ancelotti, na da yakinin cewar akwai abubuwa masu kyau tafe nan gaba kadan. Ya kara da cewar za’a ga hazakar ‘yan wasan shi nan ba da jimawa ba, don a shirye suke.