Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Shiga Muhawara A Kan Yadda Jam'iyyu Zasu Iya Samar Da Ayyukan Yi Yau Jumma'a


Ku Shiga Muhawara A Kan Yadda Jam'iyyu Zasu Iya Samar Da Ayyukan Yi Yau Jumma'a

Kuna iya kiranmu a kan +12025486630 ko ku aiko mana da Email na tambayoyinku domin shiga wannan muhawara da Sashen Hausa na Muryar Amurka da gidan rediyon Freedom FM dake Kano suka shirya

Masu sauraro, a yau jumma’a, sashen Hausa na Muryar Amurka da gidan rediyon Freedom FM dake Kano, zasu dauki muhawara a tsakanin manyan jam’iyyun dake takara a zabe kan yadda zasu samar da ayyukan yi ga jama’a.

Idan mai sauraro yana so, zai iya aiko mana da tambayarsa kan yadda jam’iyyun zasu iya samar da ayyukan yi ta hanyar Email, zuwa ga sashenhausa@voanews.com ko kuma ta hanyar cike takardar tuntubarmu a wannan dandalin.

Haka kuma ana iya kiranmu a lokacin da muke daukar wannan muhawara da karfe 6 na maraice agogon Najeriya a kan +12025486630.

Yau Jumma'a da maraice, daga karfe 6 zuwa 7 agogon Najeriya. Sai mun ji ku

XS
SM
MD
LG