Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwallon Kafar Manchester United Tace A Shirye Take

Kungiyar Manchester United A shirye take.
Kungiyar Manchester United A shirye take.

Kungiyar kwallon kafar Manchester United ta kasance ta 4 a jerin kungiyoyi na wasan Firimiya lig, ita dai kungiyar tana so ta tsaya a wannan matsayin a dai dai lokacin hutun karshen shekara.

Dan wasannan Michael Carrick ya bukaci ‘yan wasan Manchester United da su cigaba da rike wuta duk dacewar wannan lokacin hutun kirismas ne.

Bayan fara wannan kakar cikin wuya, Louis Van Gaal ya cinye wasanni 5 cikin wasanni karshe 8 da suka buga, wanda ya kaisu ga mataki na 4 a tebur.

Babar nasararsu dai tasamu ne a sanadiyar dawowar dan wasa Carrick, wanda shi yayi sanadiyar cin wasansu 3-0 ranar Asabar.

Shidai dan wasan tsakiya yana sa ran kungiyar tasu zata cigaba da lokacinta, za kuma su buga wasa ranar Talata da kungiyar Stoke City.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:50 0:00
Shiga Kai Tsaye


  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG