WASHINGTON, DC —
A shirin A Bari Ya Huce na wannan makon zaku ji labarin wani dattijo Bafullatani mai bakar rowa. Ganin baya banbaro ya'yanshi suka yi shawara su gayyaci malami ya yi mashi kashedi kan illar wannan halin amma a karshe duka hakarsu bata cimma ruwa ba.
Mun kuma yi hira da mawakin nan da ake kira kwamanda, wanda ya shiga sana'ar waka bayan ya yi ritaya daga aikin soja
Saurari cikakken shirin.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.