Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Gidan Radiyo Sun Fara Yajin Aiki

Dakin Watsa Labarai
Dakin Watsa Labarai

Kafofin yadda labarai mallakar Gwamnatin jihar Neja, sun fara wani yajin aiki, na har sai abun da hali yayi wanda ya hada da ma’aikatan kafofin labaran da masu wasan kwaikwayo, da ake kira RATTAWU.

Wannan alamari dai ya jefa daruruwan mutanen jihar dake amfani da kafofin yada labaran cikin wani hali na rashin jin komai daga wadannan kafofin yada labarai.

Shugaban kungiyar ma’aikatan na RATTAWU, a jihar Neja, Komrade Sadiq Muhammad Aliyu, yace makasudin wannan yajin aikin sine saboda kin biyansu sabon tsarin albashi da shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya sanya wa hanu tun shekaran 2012, wanda a cewarsa su a yanzu ba batun kudade na baya sukeyi ba, amma fara biyan su da sabon tsarin albashin.

Shugaban yace sun sha zaman yin taro da shugaban ma’aikata na Gwamnatin jihar Neja, na tsawon shekaru biyu har yanzu babu wani alamun cewa za’a aiwatar da sabon tsarin.

Yajin aikin Rattawu - 2'57"

No media source currently available

XS
SM
MD
LG