Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magajin Gari MIchael Bloomberg Ya Yaba Ma 'Yan Sandan Birnin New York


'Yan sanda dake ci gaba da binciken yunkurin tayar da bam cikin mota a a daren asabar sun ce ba su ga shaidar akwai hannun Taliban ba tukuna, duk da ikirarin kungiyar dewa ita ce ta yi kokarin kai harin.

Magajin garin birnin New York, Michael Bloomberg, ya yaba ma rundunar 'yan sandan birnin a saboda matakan da ta dauka da gaggawa dangane da wani yunkurin tayar da bam cikin mota da daren asabar a dandalin Times Square.

Magajin garin yayi magana da 'yan jarida daren lahadi, jim kadan kafin ya shiga cikin wani gidan abinci dake dandalin na Times Square inda suka ci abinci tare da Wayne Rhatigan, dan sandan da ya fara kawar da mutane a kusa da inda motar take a daren asabar.

Wasu mutane biyu masu talla a gefen hanya, wadanda dukkansu tsoffin sojoji ne, su ne suka kira wannan dan sanda suka nuna masa motar a bayan da suka ji wata kara suka kuma ga hayaki na fitowa daga cikin wannan motar Jif kirar Nissan Pathfinder wadda aka ajiye a gefen hanya.

Bloomberg ya ba da tabbacin cewa akwai tsaro ga lafiyar jama'a a New York, inda ya lura da cewa dandalin na Times Square, cibiyar gidajen wasannin kwaikwayo na Broadway, da gidajen sinima da gidajen cin abinci, ya sake cika makil da jama'a a lahadin nan. Yace birnin New York na da "rundunar 'yan sandan da ta fi kowace iya aiki a duniya" ya kuma roki fararen hula da su kwantar da hankula bisa sanin cewa 'yan sandan zasu yi aikinsu yadda ya kamata.

'Yan sanda sun kwashe dubban 'yan yawon shakatawa da masu zuwa kallon wasannin kwaikwayo ko sinima daga wannan yanki a daren asabar, a yayin da suke kokarin dauke wannan mota da abubuwan dake cikinta, wadanda suka kai wani wurin domin gudanar da bincike. An sake bude wannan unguwa ga jama'a da safiyar lahadi.

'Yan sanda sun ce ba su ga shaidar hannun Taliban a yunkurin kai harin na bam a cikin mota ba, duk da ikirarin da wata kungiya a Pakistan ta yi.

Kwamishinan 'yan sanda na New York, Ray Kelly, ya fadawa 'yan jarida cewa an ga wani mutumin da ake zaton shi ne ya ajiye motar a cikin faifan bidiyo na kyamarorin da suke kunne dare da rana su na daukar hoto a birnin, amma har yanzu 'yan sanda ba su yi magana da shi ba.

Tun fari, magajin garin New York Bloomberg yace motar da aka yi niyyar kai harin da ita tana dauke da tankokin gas guda uku, da kayan wasan wuta, da jarkoki biyu cike da man fetur, da kuma agogo guda biyu da baturorinsu. Yace da alamun duk wanda yayi niyyar hada wannan bam dan koyo ne, amma kuma yace da wadannan tarkace sun kama, to da zasu iya yin barna.

Wani kakakin 'yan sanda, Paul Browne, yace an ga alamar wannan bam din ya fara kamawa, amma sai ya mutu.

XS
SM
MD
LG