Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai da ta Dattawan Najeriya Bakinsu Yazo Daya

Majalisar Najeriya
Majalisar Najeriya

A karshen watan Oktoban, da ya gabata ne Majalisar Tarayyar Najeriya, ta aike da daftarin kundin tsarin mulkin Najeriya, ga majalisar jihar Kano kamar yanda ta mika shi ga sauran majalisun dokokin jihohi.

Tuni dai majalisar wakilai da takwararta ta Dattawan Najeriya, bakinsu yazo guda, game da sassan da za’a yiwa kwaskwarima, kuma tilas ne zai kashi biyu bisa uku na yawan majalisun jihohi, sun amince da gyare-gyaren, kafin a tabbatar dasu.

Tun farkon wannan shekaran ne aka nemi ra’ayin ‘yan Najeriya, game da sassa da kuma batutuwan da ake da muradin shigarwa ko ayimasu kwaskwarima, a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Baya ga jin ra’ayoyin jama’a. akwai kudirorin, da wakilan taron kasar da akayi suka cimma, wadanda suma akeso a shigar dasu cikin sabon kundin.

Majalisar Dokokin Kano 3'14"

No media source currently available

XS
SM
MD
LG