Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Aure Dake Koyaswa Sun Kai Kukansu Wajen Shugabannin Addini A Nijar

Shirin mahukumtan kasar Nijar na kai matans aure malaman makarantun firamare aiki karkara ba tare da yin la'akari da aurensu ba ya sa sun harzuka sun soma zaman dirshan tareda kai kokensu wa hukumar addinin Musulunci ta kasar domin su shafe masu hawaye

Mahukuntan harkokin ilimin firamare a jamhuriyar Nijar sun kuduri aniyar rage cunkoson malamai a birane musamman a birnin Yamai. Sabili da haka suka yi yunkurin sakewa wasu malaman da suka hada da dubban matan aure guraben aiki zuwa karkara daga Yamai.
Matan sun koka domin jefasu karkara na nufin zasu bar mazajensu na aure a birnin Yamai ke nan, lamarin da suke ganin ya sabawa shirin iyali da addinin Musulunci. Domin samun masalaha sun shiga zaman dirshan tare da kai kokensu zuwa hukumar shugabannin addini dake kula da shirin iyali a kasar ta Nijar

Domin Kari

XS
SM
MD
LG