WASHINGTON, DC —
Kungiyar Gwamnoni arewa tare da hadin gwiwar gidauniyar, tunawa da Sardaunan Sokoto, sir, Ahmadu Bello, sun tallafawa matan jami’an tsaron da aka yiwa kisan gilla a garin Alkiyo, dake jihar Nasarawa, da kudi Naira Miliyan, 34.
A bara kungiyar, Gwamnonin, tayi alkawarin tallafawa marayun da iyayensu mata, da kudi Naira Miliyan 100, domin kyautata masu rayuwa.
Sakatariyan, Gwamnatin jihar Nasarawa, Hajiya Zanaib Ahamad,ta yaba da tallafin, takuma yi kira dasu cika sauran alkawarin.Ta kara da cewa an raba kudin daidai inda kowace mace ta sami fiye da Naira dubu dari hudu.