Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Kada ku Rena Sana'a Komi Karancin Jari

Matasa kukama sana'a
Matasa kukama sana'a

Matasa kuka ma sana’a kowace iri kuma kada ku renan sana’a. Wani matashi me sana’ar saida motoci kenan yayi wannan kiran a wani zantawa da mukayi da shi. Ya shai da mu na cewar ya fara wannan sana’ar tun yana dan makarantar sakandire kamin ma yayi tunanin mai zai zamo a rayuwashi. Kuma wannan sana’ar ya fara tane a sanadiyyar zama da yake yi da masu wannan sana’ar, ta nanne yasamu sha’awar wannan harka.

Ya yi nuni ga matasa da su tashi su kama sana’a a kowane irin halin rayuwa suka samun kansu, don tahaka ne kawai zasu iya zama wani abu a rayuwa. Kuma babbabn abun la’akari dashi a nan shine kada su bar karatu, don ya kasance yana wannan sana’ar amma kuma bai bar karatuba, saboda karatu na da matukar mahimanci, don a lokutta da dama wasu abubuwan bazaka iya yinsu ba har sai kanada ilimi.

Yayi nuni da cewar a kowace irin sana’a ko hali nayau da kullun akwai matsaloli da mutun zai iya fuskanta, sai dai mutun yayi kokarin ya fi karfin zuciyar shi da kuma tunanin kome nene a rayuwa zai iya shi idan har yasakan shi. Kuma karatu ko sana’a babu wanda ke hana wani yuwa, sai kawai mutun yayi kokari a kowane irin hali ya samu kanshi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG