Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawakiya Tiwa Savage Ta Shigar Da Karar Mawaki Davido Kan  Zargin Barazana Ga Rayuwarta


Tiwa Savage (Hoto: Shafin Instagram na Tiwa savage)
Tiwa Savage (Hoto: Shafin Instagram na Tiwa savage)

Shahararriyar mawakiyar Najeriya kuma marubuciyar waka, Tiwatope Omolara Savage, wacce aka fi sani da Tiwa Savage, ta kai kara ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Fayoade Adegoke, kan fitaccen jarumin nan mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido.

Lamarin ya samo asali ne daga barazanar da Tiwa Savage ke zargin Davido da yiwa rayuwarta biyo bayan wata musayar cece-kuce da ya wakana a kafafensu na sada zumunta, sakamakon wallafa wani hoto da tayi a kafar sada zumunta.

Rikicin ya samo asali ne bayan Tiwa Savage ta wallafa wani hoto a Instagram tare da Sophia Momodu, tsohuwar budurwarsa ta mu’amala da suke da suke da zuri’a a tsakanin su.

Mawakiyar ta cigaba da bayyana sakon da Davido ya aika mata na gargadi da zargi na keta mutunci, ta jaddada yadda alakar su da mutunta juna da abokanta ta kasance a baya wanda ya hada da taimakekeniyar juna alokacin tsanani da wahala.

Tiwa ta bayyana matukar damuwarta na zargin cin zarafi da zai iya aukuwa da ita a yanar gizo harma da rayuwarta na yau da kullum a zahirance, inda ta bayyana dora alhakin hakan kan mawakin kan duk wata cutarwa da kan iya samun ta ko iyalanta.

A cikin karar, Tiwa Savage ta bukaci kwamishinan ‘yan sandan da ya tuhumi Davido kan duk wata illa da za ta iya fuskanta.

Takardar koken ta ce, "Na rubuto ne domin in bayyana muku yanayin da nake ciki a halin yanzu cike da damuwa da ya shafi kaina, Tiwatope Omolara Savage wanda aka fi sani da Tiwa Savage, da Mista David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido."

Rikicin da ke tsakanin mawakan biyu ya fito fili ne a ranar 6 ga watan Janairu, lokacin da suka daina bin juna a shafukan su na Instagram, duk da abokantakar da suka yi a baya da kuma abubuwan da suka faru tsakanin ‘ya’yansu.

Lamarin da ya janyo cece-kuce iri-iri da nuna damuwa a shafukan sada zumunta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da sahihancin koken, yana mai cewa, “Gaskiya ne”. Koken Tiwa Savage, kamar yadda aka zayyana a cikin koken, ta yi zargin Davido da nuna rashin da’a da kuma yi mata barazana kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokokin aikata laifuka ta yanar gizo suka tabbatar.

Lamarin ya dau hankalin mabiyan mawakan biyu matuka, inda da dama suke nuna damuwarsa, a dayan bangaren kuma kowannen su na goyon bayan mawakinsa.

~Yusuf Aminu Yusuf ~

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG