Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mexico Zata Kara da Brazil

Mexico da Najeriya
Mexico da Najeriya
Kungiyoyin wasan kwallo kafa na shirye-shiryen buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, inda suke ta buga wasanin sada zumunta tsakaninsu.

Kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Mexico ta nunawa kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Iziraila,cewa ruwa ba sa’an Kwando bane inda ta lallasa ta da cin uku da babu,a wani wasan sada zumunta da suka buga.

A ci gaba da shirin da take yi kungiyar wasan kwallon kafa ta Mexico, zata kara da Equador a wasan sada zumunta, ranar asabar a Arlington jihar Texas ta kasar Amurka.

Zata kuma kara da Bosnia Herzegovina, ranar talata a birnin Chicago,sa ilinan ta hadu da Kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Portugal a mako mai zuwa ranar shida ga watan gobe a garin Massachusetts.

Mexico, zata kara da kasar Kamaru, a wasan ta na farko a gasar cin kofin kwallo na duniya na bana,zanan ta kara da kasar Brazil bayan kwanaki hudu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG