Mutune da yawa sun rasa rayukansu bayan an kammala wasa tsakanin Kamaru da Comoros a ranar Litinin da yamma. Kamaru ta yi nasara kan Comoros, amma nasarar mai ɗaci.
A karshen wasa tsakanin Kamaru da Comoros, mutun 8 daga cikin' yan kallo sun rasa rayukan su, inda wasu da dama suka jikkata a sanadiyar cunkoso da aka samu wajen fitowa daga filin wasa.