Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Yi Babban Rashi a Rayuwata – Ali Jita


Mawaki Ali Jita

Fitaccen mawaki Ali Jita a masana'antar Kannywood da ke arewacin Najeriya, ya ce rasuwar mahaifinsa babban rashi ne a rayuwarsa.

Mahaifin Ali ya rasu ne a ranar Juma’a.

“Mahaifina ya rasu a daren jiya (Juma’a), na yi rashi babba, na san cewa zan yi kewarsa sosai.”Ali Jita ya rubuta a shafinsa na Instagram.

Cikin sakon na Instagram Ali wanda sabbin wakokinsa na “Mai Waka” da “Call On Me,” suke tashe a ‘yan kwanakin nan ya kara da cewa, “mahaifina mutum ne jarumi da ban taba ganin irinsa ba, ina maka fatan Allah ya ba ka Jannatul Firdaus, Allah ya sa karshen wahalarka kenan.”

Tuni dai da yawa daga cikin abokanan sana’arsa a ciki da wajen masana’antar Kannywood suka mika sakon ta’aziyyarsu ga mawakin.

“Allah ya jikan sa da rahama, ya sa ya huta, Allah ya sa jinya ta zamo kaffara. Allah ya ba ku hakuri da dangana, Ameen.” Fitaccen jarumi Sani Mu’azu ya ce.

“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Allah ya jikan sa da rahama. Ameen!” Jaruma Rahama Sadau ta rubuta.

Takwaran sana’arsa, mawaki Lilin Baba cewa ya yi, “Allah ya jikan sa da rahama dan uwa.”

Baya ga wadanda suka mika sakonnin ta’aziyyarsu ta shafinsa, sauran jaruman Kannywood irinsu Ali Nuhu, Adam A. Zango sun wallafa ta’aziyyarsu a shafukansu na Instagram.

“Muna addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa ya sa Aljanna ce makomarsa.” In ji Adam a Zango.

“Muna addu’ar Allah ya jikan sa ya gafarta masa, mu kuma idan ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da imani.” In ji Ali Nuhu.

Rasuwar mahaifin Ali Jita na zuwa ne kasa da mako biyu bayan rasuwar mahaifin jarumi Ibrahim Maishunku.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG