Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya An Yi Biki Da Tsoro

'Yan Najeriya dake arewa maso gashin kasar, mahaifar kungiyar Islama mai tsatsauran ra'ayi sun yi bikin karamar sallah ranar Alhamis da addu'o'i cikin murna da annashuwa da gaisuwar bangirma da jama'a fiye da 10,000 suka kaiwa Shehun Borno a fadarsa. Cikin shekaru uku da suka gabata ba'a iya yin hawan daba ba sai wannan shekarar lamarin da ya cika mutane da murna a duk fadin birnin Maiduguri. Kodayake akwai tsauraran matakan tsaro amma an ji mata na guda suna ihun jin dadi da yara da manya kuma suna wakoki suna yiwa shehunsu fatan tsawon rai.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG