Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya da Argentina Sun Sake Kasancewa Cikin Rukuni Daya a Gasar Cin Kofin Duniya Na Shekarar 2014

Hukumar Kwallon Kafa Ta Duniya ko FIFA a takaice ta yi bikin sanarda jadawalin wasan cin kofin duniya na shekarar 2014 a garin Costa do Sauipe a Brazil ranar 6 ga watan Disambar 2013.

Jadawalin ne ya bayyana kungiyoyin da zasu kara da juna a gasar kwallon kafa na bazara mai zuwa. Argentina da Najeriya suna rukuni daya na F kamar yadda aka hadasu a wasan da aka yi a Korea da Japan a shekarar 2002 da kuma Afirka Ta Kudu a shekarar 2010. Dama akan sa wadanda suka saba gasa da juna su biyu tare da sabbin zuwa biyu kamar Bosnia da Herzegovina da Iran.

XS
SM
MD
LG