Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nigeria Election Blast


Abokan hamayyar shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan sun zarge shi da amfani da kazamin harin bom da aka kai makon jiya wajen yi masu barazana yayinda zabe ke karatowa. Tsohon shugaban mulkin soja a kasar Ibrahim Babangida wanda ake gani a matsayin babban abokin hamayyar Mr. Jonathan a takarar share fage na jam’iyar PDP mai mulki, da kuma wadansu ‘yan takara uku sun sa hannu a wata sanarwa suna zargin shugaban kasar da bita da kullin siyasa. Farko wannan makon aka kama shugaban kamfen Babangida Raymond Dokpesi, aka yi mashi tambayoyi dangane da harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 12. An sake shi daga baya, sai dai yana ci gaba da fuskantan Karin tambayoyi. Ba a danganta Babangida da hare haren ba.Kungiyar tsageran yankin Niger Delta Movement for the Emancipation of Niger Delta MEND ta dauki alhakin harin. Tun farko, shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan yace kungiyar bata da hannu a harin. Ya bayyana cewa ana amfani da sunan kungiyar ne domin cimma wata manufa da aikata miyagun laifuka.

XS
SM
MD
LG