Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nura Na Gwanja: Waka Ce Mafi Sauki Cikin Hanyoyin Isar Da Sako


Nura Muhammad

A shirinmu na Nishadi, wakiliyar VOA Hausa ta yi hira da mawaki Nura Muhammad Inuwa wanda aka fi sani da Nura LOC ko Nura na Gwanja.

Nura ya ce sana'arsa ita ce sayar da babura a hannu guda, kuma malamin makaranta ne, sannan a wani yunkuri mai dogaro da kai, har ila yau kuma yana waka domin nishadantarwa, da kuma fadakarwa.

Nuran Gwanja ya ce, ya shafe shekaru 9 yana waka, sannan ya fara waka ne tun makarantar Islamiya inda yake wakokin ban kwana wa mata da suka yi aure.

Ya ce babban jigonsa a masana’antar nishadi ba wani ba ne illa Ado Gwanja, sakamakon yana nishadantarwa da fadakarwa ta hanyar nishadi, inda yakan isar da sakon da ya dace.

Ya ce kamar kowanne mawaki, yana fama da rashin fahimta daga bangaren al’umma inda ake yi masa kallon abin da ya ke yi, ma’ana harkar waka, maimakon ya kara tarbiya, da karatu, yana haifar da tabarbarewar al’ada da tarbiya ne a cikin al’umma.

Nuran Gwanja ya ce wakar ita ce hanya mafi sauki da ke isar da sakon shafin sadarwa na zamani, alal misali a wata wakarsa da ya yi, na yadda mata ke kashe mazajensu a yanzu, wakar ta taimaka ainun wajen isar da illar yin hakan.

Ga cikakken rahoton hirar daga wakiliyar DandalinVOA Baraka bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:37 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG