Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pastore Yace In PSG Ta Yi Sake, Chelsea Zata Yi Mata Sakiya - 3/4/2014


Manajan kungiyar PSG ta Faransa, Laurent Blanc
Manajan kungiyar PSG ta Faransa, Laurent Blanc
Dan wasan kungiyar Paris Saint Germain (PSG), Javier Pastore, ya ce bai kamata kungiyarsa ta yi sakaci ba, duk da cewa ta doke Chelsea da ci 3-1 a gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai karon farko da suka yi jiya laraba.

Pastore yace wasan da zasu yi a mako mai zuwa, a gidan ‘yan Chelsea, wasa ne da ya kamata su dauka da matukar muhimmanci, domin Chelsea ba kanwar lasa ba ce duk da doke ta da suka yi.

Pastore yace in sun yi sake, to Chelsea tana iya yi musu sakiya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG