Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Maganin Rigakafi Ya Rage Ci gaban Da Aka Samu A Shawo Kan Illar Kyanda

Wata yarinya mai fama da cutar kyanda
Wata yarinya mai fama da cutar kyanda

An sami raguwar kananan yara dake mutuwa ta dalilin kamuwa da cutar kyanda da kusan kashi 75% a duniya tun shekara ta 2000, sai dai rahotanni na nuni da cewa, an sami karuwar bullowar cutar a Asia da jijohin Africa sakamakon rashin allurar rigakafi dayta rage wannan ci gaban kawar da cutar.

Rahoton da Kungiyar lafiya ta duniya ya bayar ya yi nuni da cewa, wannan cuta mai yawan yaduwa itace kan gaba a wajen mutuwar kananan yara a duniya gaba daya, musamman talakawa, marasa abinci mai kayan gina jiki da kuma marasa rigakafi.

An sami nasarar shawo kan bakon dauro a kasashen arewaci da kudancin Amurka, yayinda kuma yammacin sashin Pacific suna kan hanyar kawar da shi, amma yammacin Turai na baya wajen haka domin rashin allurar rigakafi, bisa ga bayanin majalisar dinkin duniya.

Rahoton ya nuna cewa, an sami karuwara yaduwar wannan cutar a kasashe da dama da suka hada Demokaradiyar Congo, India da Nigeria.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG