Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Bauchi Ya Nemi a Kafa Dokar Tilasta Rigakafin Polio


Sabon Sarkin Bauchi, mai martaba Muhammad Rilwanu Sulaiman, yana ganawa da dan'uwansa Muhammad Nasiru Sulaiman
Sabon Sarkin Bauchi, mai martaba Muhammad Rilwanu Sulaiman, yana ganawa da dan'uwansa Muhammad Nasiru Sulaiman

Mai Martaba Rilwanu Sulaiman Adamu, ya fada a wani taron da VOA ta shirya cewa kafa dokar tilasta yin rigakafin Polio zata taimaka wajen dakile yaduwarta a cikin jihar.

A wani mataki na dakile yaduwar cutar shan inna ta Polio, Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu, yayi kira ga gwamnatin jihar da ta nazarci yiwuwar kafa dokar tilasta yin rigakafin Polio.

Sarkin na Bauchi, ya yi wannan kiran ne a cikin kasidar da Dan Amar na Bauchi, Alhaji Hassan Bayero, ya gabatar a madadinsa a wurin taron yaki da cutar Polio wanda Muryar Amurka da kuma Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu yaduwa ta Amurka suka shirya a Bauchi.

Yace yin hakan zai tilasta ma iyayen dake kin yarda su samarwa da ‘ya’yansu wannan kariya ta rigakafin su karbi wannan magani mai muhimmanci.

Yace koda yake an samu raguwar wannan cuta sosai, akwai bukatar kafa dokar da zata iya hukumta iyayen da suka ki ba ‘ya;’yansu kariya.

Amma kuma sarkin na Bauchi yayi kiran da a daina yin amfani da yaran da shekarunsu bas u kai na balaga ba a matsayin masu aikin bayar da rigakafin, abimnda a can baya ya sa wasu iyaye suka ki yarda a diga ma ‘ya’yansu wannan maganin.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG