Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekara Daya Da Rabi Ba A Samu Bullar Polio A Sokoto Ba - In Ji Wamakko


Gwamna Aliyu Mgatakarda Wamakko na Jihar Sokoto yace kudurin gwamnati da na wadanda abin ya shafa ya sa aka cimma wannan tazara

Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko na Jihar Sokoto ya bayyana cewa yanzu watanni 18 ke nan, ko kuma shekara daya da rabi, ba a samu bullar cutar Polio a cikin jihar ba.

A lokacin da yake kaddamar da shirin karshe na wannan shekara na bayarda maganin rigakafin cutar ta shan inna mai gurguntawa ko kashe yara a Tureta, gwamnan na Sokoto yace kudurin gwamnatin jihar da dukkan wadanda wannan lamari ya shafa, shi ne ya kai ga samun irin wannan nasara.


Kwamishinan kiwon lafiya na Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, wanda ya wakilci gwamnan, yace gwamnati ba zata yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da kawar da wannan cuta baki dayanta daga jihar. Yace an dauki matakai da daman a tabbatar da cewa an shawo kan masu kin karbar maganin.

Shi ma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya roki dukkan sarakunan gargajiya da shugabannin addini da su tabbatar da cewa sun wayarda kan al’ummarsu game da bukatar yin wannan rigakafi.

Hakimin Bodinga, Alhaji Bello Abdul-Ra’uf shi ne ya wakilci Sultan na Sokoto a wannan taron.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG