WASHINGTON, DC —
Sabon shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya kai ziyarar shi ta farko wata kasar waje, wadda ta ba shi damar cika alkawarin shi na yin Umrah a kasar Saudiyya.
Ofishin Mr.Ghani ya fada a cikin wata sanarwa a yau Asabar cewa shugaban zai yi Umrah, sannan zai gana da Sarki Abdullah, da kuma sauran jami'an gwamnati a yayin ziyarar da ya kai kasar ta Saudiyya.
Da yake rantsuwar kama ragamar mulkin kasar Afghanistan, Mr.Ghani yayi alkawarin cewa ziyarar farkon da zai kai wata kasar waje itace ta zuwa yin Umrah a kasar Saudiyya.
Bambancin aikin Hajji da Umrah, shi ne Umrah ba lokaci, ana iya yin ta a kowane lokaci.