Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afrika Suna Babban Taro Kan Yaki Da Manyan Cututuka


Shugabannin Afrika

Shugabannin Afrika baki daya ko kuma wakilansu na halartar wani kasaitaccen taro wanda ake nazari tare da yin bita a kan yaki da cututukan nan na kanjamau da tarin fuka da malariya watau zazzabin cizon sauro da manyan cututuka dake addabar kasashen Afrika.

Shugabannin Afrika baki daya ko kuma wakilansu na halartar wani kasaitaccen taro wanda ake nazari tare da yin bita a kan yaki da cututukan nan na kanjamau da tarin fuka da malariya watau zazzabin cizon sauro da manyan cututuka dake addabar kasashen Afrika. Kasashe 10 me suka yi jawabai masu karfin gaske a rana ta farko inda suka nuna muhimmancin hada kai da kuma gamsuwar da suka yi da kuma tabacin cewa, zasu tabbatar sun hada karfi da karfe domin a yaki wadannan cututukan daga cikin Afrika.

Kamar yadda shugabannin suka nuna ana sa ran lallai za a fito da cibiyoyi dabam dabam wadanda zasu yi nazari tare da binciko magungunan da Afrika da kanta zata kirkiro domin yaki da wadannan cututukan koma a aika da su kasashen keatare domin ciniki a kansu.

Daya daga cikin manyan jami'an da suka shirya wannan taron a shekara ta 2011, Professor Abdulsami Nasidi tace an sami ci gaba ya kuma bayyana muhimmancin taron na bana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG