Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Taliban Sun Kai Farmaki A Yunkurin Wargaza Taron Neman Zaman Lafiya


'Yan Taliban sanye da rigunan kunar-bakin-wake da rokoki sun kai farmaki da nufin wargaza wani muhimmin taron neman zaman lafiya a babban birnin Afghanistan, a yayin da shugaba Hamidu Karzai yake kokarin neman hanyar warware rikicin kasar.

‘Yan Taliban sanye da rigunan kunar-bakin-wake da rokoki sun kai farmaki da nufin wargaza wani muhimmin taron neman zaman lafiya a babban birnin Afghanistan, a yayin da shugaba Hamidu Karzai yake kokarin neman hanyar warware rikicin kasar.

An ji karar harbe-harbe da fashe-fashe yau laraba a birnin Kabul, abinda ya katse jawabin da shugaba Karzai yake yi a lokacin ga wakilai su dubu daya da dari shida (1,600) da suka taru domin fara taron na kwana uku da ake kira Jirga a harshen kasar.

Jami’an Afghanistan sun ce dakarun tsaro sun harbe, suka kashe ‘yan harin kunar-bakin-wake akalla biyu wadanda suka yi shigar mata su na kokarin kutsawa cikin inda ake taron. Suka ce an kama wani dan tsageran na uku.

Shugabannin Taliban sun dauki alhakin kai harin. Ba a samu rahoton mutuwa ko jin rauni a tsakanin wakilan taro ko kuma farar hula ba.

A lokacin da yake jawabi gaban taron, shugaba Karzai ya mika hannun abota ga ‘yan Taliban yana mai rokonsu da su daina lalata kasarsu su komo cikin al’umma. Karzai yace dukkansu ‘yan’uwa ne, kuma akwai bukatar su kawo karshen irin wannan kashe-kashe. Amma kuma ya kara da cewa ba za a yafe ma ‘yan al-Qa’ida ko kuma wadanda suka kashe fararen hula ba.

XS
SM
MD
LG