Bisa al’ada, kowace sabuwar gwamnati a Amurka ta na bullo da manufofi a game da yadda huldarta da kasashen Afirka za ta kasance. Jami’an gwamnatin Joe Biden sun kyankyasa cewa wannan taro, zai bude wani sabon babin kawance tsakanin Amurkar da nahiyar.
Taron Kolin Amurka Da Afrika: Amurka Ta Ce Za Ta Sauya Yadda Take Hulda Da Afirka