Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Neman Zaman Lafiya A Jihar Zamfara

Jihar Zamfara ta kwashi shekaru da dama tana fama da kashe kashen mutane da sacesu da kuma satar shanu duk da dimbin sojoji da sauran jami'an tsaro da aka tura jihar

Ganin cewa duk wani kokari na yin anfani da karfin sojoji da na 'yansanda ya cutura ya sa gwamnatin jihar tayi tunanen neman sasanta bangarorin dake kai ma juna hari suna kashe kansu.

Wani kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ya bi duk masarautun jihar da kananan hukumomi tare da bin sawun shugabannin Fulani da wasu kungiyoyin jama'a da zummar shawo kansu.

Nasarar da kwamitin ya samu ya sa gwamnati ta shirya taron duk masu ruwa da tsaki a lamarin tare da sarakuna da shugabannin al'umma da kungiyoyin sa kai domin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya a duk fadin jihar

Domin Kari

XS
SM
MD
LG