Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Zaman Tattaunawa Akan Cutar Polio a Jihar Borno

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya gudanar da taron tattaunawa da iyaye mata akan cutar Polio, a birnin Maiduguri dake jihar Borno. Jummai Ali daga sashen Hausa ita ce madugun tattaunawar, inda ta zanta da iyaye mata, jami’an kiwon lafiya da shuwagabanni domin karin haske, da fahimta akan illar wannan cuta, da muhimmancin yaki da ita. An gudanar da tattaunawar ne a gidan radiyo da talabijin din Borno ran 13 ga watan nan na Mayu. Najeriya dai tana daga cikin kasashe uku kacal a duniya, da har yanzu ke dauke da cutar polio.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG