Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakar Tiwa Savage Ta Shiga Jerin Wakokin Fim Din “Coming To America 2” 


Tiwa Savage (Hoto: Daga shafin Instagram na Tiwa savage)
Tiwa Savage (Hoto: Daga shafin Instagram na Tiwa savage)

An saki jerin sunayen wakokin da za su fito a sabon fim din "Coming To America 2" da ake shirin haskawa a watan Maris.

Yayin da ranar da ake shiri sakin fim din “Coming To America 2” ke kara karatowa, an saki jerin wakokin da za a ji su a cikin fim din wanda aka yi wa kundin da taken “Rythms of Zamunda,” kuma wakar fitacciyar mawakiyar Najeriya Tiwa Savage ta samu shiga wannan kundi.

Wakar Tiwa mai suna “Dangerous Love” ita za ta fito a fim din, wanda ake shirin sakarsa a ranar 5 ga watan Maris.

Wani fitaccen mawaki da shi ma wakarsa za ta fito a fim din shi ne Tekno da wakarsa ta “Skeletun.”

Kundin mai dauke da wakoki 16 ya tattaro mawakan Afirka da dama da suka hada da Larry Gaaga, Umu Obiligbo, Nasty C, Prince Kaybee da Fally Ipupa da suka fito daga kasashen nahiyar.

Baya ga Najeriya, sauren kasashen Afirkan da mawakansu za su fito sun hada da Cote d’Ivoire, Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a wannan fim din da Craig Brewer ya ba da umurni.

Shirin “Coming To America 2” fim ne da zai kasance ci gaban “Coming To America” na farko da aka yi a shekarar 1988 wanda ya kunshi labarin Yarima Akeem na masaruatar Zamunda (Eddie Murphy) da ya kai ziyara Amurka shi da aminisa Arsenio Hall don neman matar da zai aura.

A wannan jukon, Akeem, zai sake komawa Amurka inda zai je neman dansa da aka haifa masa a wancan ziyarar farko da ya kai.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG