Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Najeriya Harrison Odjegba Okene an Cetoshi Bayan Ya Kwashe Kwanaki Uku a Makale Cikin Ruwa

Okene yana aiki ne a matsayin mai dafa abinci cikin wani jirgin ruwa a gefen tekun Najeriya tun watan Yunin shekarar 2013. Yayin da wata muguwar guguwa ta taso kan teku sai jirginsu ya kife ya kuma nitse inda 'yanuwansa ma'aikata goma sha daya suka rasu amma shi Okene ya samu wani mafitar iska a jirgin wanda ya rike har ya yi kwana uku kafin wata kungiyar masu ceto daga Afirka Ta Kudu ta cetoshi.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG