Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Nijar 9


Sojojin Kasar Nijar
Sojojin Kasar Nijar

A jamhuriyar Nijar yayin da aka fara ganin alamun lafawar hare haren ta’addanci a ‘yan makwanin nan akan iyakar kasar da Mali, jiya alhamis wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan jami’an tsaron Jandarma da Garde nationale a barikin Ayorou da ke kilomita 180 da arewa maso yammacin birnin Yamai inda suka yi nasarar hallaka a kalla 9 daga cikinsu tare da jikkata wasu.

Rahotanni daga mazauna garin na Ayorou sun bayyana cewa a wajajen karfe 1 na ranar alhamis ne wasu ‘yan bindiga akan babura wadanda ba a tantance yawansu ba suka afkawa jami’an tsaro cikin wani yanayi na bazata.

Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dakarun Nijar 9 sannan sun jikkata wasu da dama kamar yadda wani wanda ya sheda lamarin ya bayyana wa wakilinmu Souley Mummini Barma.

Ministan cikin gida a kasar Bazoum Mohamed a shafinsa na twitter ya tabbatar da cewa an kaiwa jami’an tsaron harin.

Yana mai jinjina wa dakarun tsaron kasar saboda a cewarsa sun nuna jarumta a yayin wannan lamarin haka kuma ya nuna gamsuwa da nasarorin da aka samu biyo bayan samamen rundunar Barkhane.

Wannan hari na zuwa ne kwanaki kadan bayan da mayakan boko haram suka kai farmaki a barikin sojan Chetimari dake yankin Diffa inda suka kashe askarawa kimanin 8, kafin daga bisani sojan saman Nijar su ka yiwa maharan luguden wuta a dai-dai lokacin da suke shirin ketara iyaka inji wata sanarwar gwamnati.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG