Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Afirka Sun Hada Kai Don Goyon Bayan Ghana


'Yan Afirka Sun Hada Kai Don Goyon Bayan Ghana

Jami'an Afirka ta Kudu sun fara rarraba tutar Ghana, yayin da kafofin nahiyar suka bukaci kungiyar Ghana ta canja suna zuwa "Black Stars" ta Afirka.

Masoya kwallon kafa a kasar Afirka ta Kudu da kuma fadin nahiyar Afirka sun hada karfi wuri guda domin su goyi bayan Ghana, kasar Afirka kwaya daya tak da ta rage a gasar cin Kofin Kwallon Kafar Duniya ta 2010 da ake yi yanzu.

Kungiyar kwallon kafa ta Ghana, wadda ake kira "Black Stars" tana fatar zamowa kungiyar wasan wata kasar Afirka ta farko da zata kai ga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya idan ta kara da 'yan wasan kasar Uruguay a wasansu na kwata-fainal ranar jumma'a a filin wasa na Soccer City dake birnin Johannesburg.

Jami'an kasar Afirka ta Kudu sun fara rarraba tutar kasar Ghana ga jama'a yayin da aka fara yin kiraye-kiraye ga kungiyar ta Ghana da ta canja sunanta zuwa "Black Stars of Arica" ko Kungiyar Black Stars ta Afirka, domin nuna irin alfaharin da 'yan Afirka suke yi da ita.

XS
SM
MD
LG