Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan kasar Yamal suna can suna murnar ficewar shugaba Saleh.


Masu hamaiya a birnin Sana'a suna murnar ficewar shugaban kasar Ali Abdullahi Saleh

yan kasar Yamal suna can suna bukuwa murna a Sanaa baban birnin kasar, bayan da labari ya bazu cewa shugaban kasar Ali Abdullah Saleh ya fice daga kasar. A ranar juma’a aka jiwa shugaba Saleh rauni a wani harin roka da aka kai fadar shugaba.

"Yan kasar Yamal suna can suna bukukuwa murna a Sanaa baban birnin kasar, bayan da labari ya bazu cewa shugaban kasar Ali Abdullah Saleh ya fice daga kasar. A ranar juma’a aka jiwa shugaba Saleh rauni a wani harin roka da aka kai fadar shugaba.

A jiya asabar aka yi jigilar shugaba Saleh da wasu jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Saudi Arabiya domin ayi musu jinya. Babu dai wani bayani da aka samu akan halin da shugaban yake ciki, kodayake rahotani sunce ana yi masa aikin tiyata. A birnin Sanaa dai mutane suna can suna ta rawa da wake wake suna ayyana cewa sun samu nasara.

To amma akwai wasu kuma da suke nuna damuwar, anya kuwa anga karshen shekaru talatin na mulkin shugaba Saleh ko kuma zai koma Yamal ne bayan ya samu sauki. Tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa mataimakin shugaba Abd Rabbo Mansour shi ya kamata ya dare kan mulki.

Tuni dai maitaimakin shugaban ya tuntunbi jakadan Amirka a Yamal Janaral Micheal Feireisten, ya kuma gana da kwamodojin kasar ciki harda iyalin shugaba Saleh. Ficewar shugaban baisa anga karshen tarzoma ba, domin a birnin Taiz wasu yan bindiga sun kaiwa fadar shugaba hari suka kashe sojoji hudu. In dai ba’a mance ba a ranar ashirin da biyu ga watan janairu aka fara wannan bore, lokacinda wasu daruruwa dalibai suka taru a jami’ar Sanaa suna bukatar shugaba Saleh ya sauka daga kan ragamar mulki, matakin da ake ganin kila zangan zangar data hambarar da shugaban Tunisia ce ta zama sanadin fara wannan bore.

XS
SM
MD
LG