Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Super Eagles Na Najeriya Sun Hallara A Nan Amurka

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Alhaji Aminu Maigari, yana jagorancin 'yan Super Eagles wadanda zasu gwabza da Mexico a Atlanta

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya su na dirar mikiya a birnin Atlanta ta Jihar Georgia a nan Amurka domin wasan sada zumunci da zasu buga da takwarorinsu na kasar Mexico.

Tuni mai horas da 'yan Super Eagles, Stephen Keshi, ya isa birnin na Atlanta domin jiran 'yan wasan nasa, wadanda a yau litinin ake sa ran zasu gama hallara a can.

Jiya lahadi tawagar shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Alhaji Aminu Maigari, ta taso zuwa Amurka tare da wasu jami'an kungiyar kamar mataimakan mai horaswa Daniel Amokachi da Ike Shorunmu.

Za a buga wannan wasa jibi laraba a babban filin wasan nan na Georgia Dome dake birnin Atlanta, kuma ana sa ran Najeriya da mexico zasu yi amfani da wannan wasan sada zumunci wajen gwada 'yan wasan da zasu buga musu a gasar cin kofin kwallon kafar duniya da za a yi bana a kasar Brazil.
XS
SM
MD
LG