Yayin da zabe ke kara matsowa, yanzu haka dai kungiyoyi da sauran al’uma na ci gaba da fadakarwa game da abunda ya kamata ‘yan Najeriya, su kula dagane da zaben dake tafe.
Kungiyoyi kama daga na muryar talaka dana rai dangin goro har na ma’abota masu sauraren kafofin yarda labarai, suna ci gaba da fadakar da jama’a, mahimmancin dake tattare da gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.
Shugaban ma’abota sauraren kafofin yarda labarai, Malam Baba Iyali Kawu, yace “kafin a zabi mutun a duba menene yayi, shine wani irin mutun ne wannan shi yakamata mutun ya tambayi kansa, ace har yanzu a Najeriya, ba’a daina kamfe da ruwa da lantarki ba.”
Shugaban ya ja hankalin matasa da kada su yarda ayi amfani dasu a matsayin ‘yan bangar siyasa, domin yin hakan shine babban alheri ga matasa, ganin cewa matasa sune kashin bayar Najeriya.