Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Amince Da Gina Masallaci A Kusa Da Inda 'Yan Ta'adda Suka Rusa Tagwayen Benaye A New York


Magoya bayan wannan shirin, cikinsu har da shugaban gundumar Manhattan sun ce yana da muhimmanci a nuna amincewa da kowane irin addini, kuma gina wannan masallacin zai karfafa guiwar Musulmi masu sassaucin ra’ayi ba irin na tsageran da suka kai harin ba.

Wata hukumar birnin New York a Amurka, ta jefa kuri’ar goyon bayan gina masallaci a wani ginin dake dab da hurumin tagwayen benayen Cibiyar Cinikayya ta Duniya, inda aka kai mummunan harin ta’addancin 11 ga watan Satumbar 2001.

A bayan da aka shafe sa’o’i ana tabka muhawara mai zafi jiya talata, wakilai 29 sun jefa kuri’ar amincewa da gina masallacin, wakili daya ya ki yarda, yayin da wasu wakilai 10 suka kauracewa jefa kuri’a.

Masu sukar lamirin ginin sun ce cin mutuncin mutanen da suka mutu ko suka tagayyara a lokacin harin ne a gina wurin ibadar Musulmi a dab da wannan wurin da Musulmi ‘yan tsagera suka lalata. Amma magoya bayan wannan shirin, cikinsu har da shugaban gundumar Manhattan sun ce yana da muhimmanci a nuna amincewa da kowane irin addini, kuma gina wannan masallacin zai karfafa guiwar Musulmi masu sassaucin ra’ayi ba irin na tsageran da suka kai harin ba.

Wannan kuri’a da hukumar ta jefa shawara ce kawai, amma ana ganinta a zaman alama ce ta irin ra’ayin al’ummar gundumar ta Manhattan.

XS
SM
MD
LG