SUDAN DA SUDAN TA KUDU

  • Ibrahim Garba

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir Mayardit, daga hagu, da takwaransa Omar al-Bashir, a birnin Juba, na Sudan ta kudu.

Shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun rattaba hannu kan wasu jerin yarjajjeniyoyi na hulda game da batun tsaro da tattalin arziki, kodayake har yanzu wasu daga cikin manyan gardandamin da suka yi kusan kai kasashen ga yaki ba a warware su ba.

Omar al-Bashir na Sudan da Salva Kiir na Sudan ta kudu sun kasance wurin bikin rattaba hannun a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha a yau dinnan Alhamis.

Yarjajjeniyar ta tanaji samar da gandun kan iyaka kebabbe dagab harkokin sojin da kuma dawo da jigilar man Kudu ta hanyoyin arewa. Wata yarjajjeniyar kuma ta tanaji kirkiro wani abin da aka kira shi ‘kan iyaka mara tsauri’ wanda zai kasance da saukin bi ga mutane, ‘yan kasuwa, dabbobi ba tare da wani sharadi ba.

Har yanzu kasashen biyu basu daidai ba kan ko way a ke da mallakar yankin Abyei mai arzikin man fetur da wasu yankunan kan iyaka. They rattaba hannu kan yarjajjeniyar cigaba da kokarin shata kan iyaka.

Da kudu da Arewa sun yi yakin basasa na tsawon shekaru 21 wanda a karshe ya kai ga samun ‘yancin gashin kan Sudan ta Kudu a cikin Yulin 2011.