Kungiyoyin fafutika sun bukaci hukumomin kasar Nijar su saki shugaban gamayyar M62 Abdoulaye Saidou, bayan tsare shi da aka yi na tsawon mako 2 bisa zarginsa da tada gobara da gangan a mahakar zinaren Tamou, sai dai masu rajin kare dimokaradiya na cewa a daina yi wa sha’anin shari’a katsalandan.
Najeriya da Nijar na ci gaba da karfafa matakan da za su bada damar gaggauta kammala shirinsu na shimfida layin dogo a aikace daga Jihar Kano a Najeriya zuwa Maradi da zai ratsa ta wasu garuruwan Jihar Katsina a Najeriya.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun cafke wasu tsofaffin shugabannin hukumar shigi da ficin kaya a ci gaba da binciken da hukumar yaki da cin hanci ta kaddamar kan wata badakalar da ta shafi dubban miliyon cfa wace ake hasashen za ta iya rutsawa da dimbin jami’an Douane, wato kwastam.
Kotun shari’ar rigingimun kasuwanci ta umurci hukumar Alhazai ta Nijar da ta mayar wa wasu maniyyata daruruwan miliyoyin cfa na kudaden da su ka biya amma kuma aka kasa kai su aikin Hajji.
Wani binciken kwararru a kasar Faransa ya gano cewa kanfanin Cominak dake hako karfen uranium a Arlit dake Jamhuriyar Nijar, ya zubar da tan milyan 20 na sinadari mai tururin guba (radioactivite) bayan ya shafe sama da shekaru hamsin yana gudanar da aikinsa a yankin.
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya bukaci kasashen nahiyar Afirka da su yi amfani da damar da ke cikin sashin gudanar da cinikayya tsakanin kasashen Afirka mara shinge (AfCFTA) don habaka kasuwancin tsakanin Afirka.
Gwamnatin Kamaru ta fada jiya Talata cewa daga ranar Larabar nan farashin man fetur zai karu da kusan kashi 15 cikin 100, biyo bayan wani sabon matsin lamba da Hukumar Bada Lamuni ta Duniya IMF ta yi game da cire tallafin man fetur.
Wasu yan bindiga sun bude wuta kan gungun mutanen da suke murnar zagayowar ranar haihuwa a wani gari a kasar Afirka ta Kudu, inda suka kashe takwas tare da raunata wasu uku, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Litinin.
Masu ruwa da tsaki a sha’anin tsara aiyukan haji da umara a jamhuriyar Nijar, sun fara gudanar da wani babban taro don nazarin hanyoyin warware tarin matsalolin da ake fuskanta shekara da shekaru.
A jawabin da tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama ya gabatar a cibiyar Chatham House da ke Landan, ya bayyana yanayin ban tausayi da Ghana ke ciki a yau, idan aka kwatanta da shekaru goma da suka gabata.
Rundunar ‘yan sandan Jamhuriyar Nijar ta kama wasu ‘yan damfara da suka hada da ‘yan Kamaru, ‘yan Jamhuriyar Benin, ‘yan Ghana, ‘yan Cote d’ivoire da ‘yan Burikna Faso da wasu ‘yan Nijar dake amfani da hanyoyin sadarwa na zamani don su tatsi kudi a hannun mutane.
Wani rahoton da reshen hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin dan adam a Jamhuriyar Nijar, UN HCHR ya fitar a yammacin ranar Alhamis, ya bayyana gano daruruwan laifukan take hakkin dan adam da aka aikata a kasar, lamarin da hukumar ta danganta da matsalolin tsaron da ake fuskanta.
Domin Kari
No media source currently available
‘Yan kasuwa a Najeriya suna rufe wuraren sana’o’insu, sannan mutane suna fuskantar kalubale wajen canja makudan tsofaffin kudinsu, akan haka muka tambayi Dr. Sa’ied Tafida, shin an ya an koyi darasi daga abin da ya faru a 1984?
Wasu dalilan da suka sa babban bankin Najeriya bullo da tsarin sauya fasalin manyan takardun kudin kasar.
Festus Okoye na hukumar INEC, ya ce su na da kyakkyawar fata akan cewa duk wadanda suka yi rijista, za su karbi katunansu, Farfesa Abdulsalam na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa ya yi mana karin haske akan haka.
Daga Jihar Bauchi a Najeriyar mun tattauna da Farfesa Abdulsalam Ya'u Gital na jami’ar Abubakat Tafawa Balewa wanda ke bibiyar yadda aikin raba katin zaben ke gudana.
A ci gaba da tattaunawarmu da Farfesa Abdulsalam Ya'u Gital game da batutuwan Zabe, ya mana karin haske akan wasu matsaloli da za su iya shafan zabukan dake tafe.
An kuma gano matsaloli da ake samu a wasu wurare na wadandan shekarunsu ba su kai ba, amma suka yi rijistar katin zaben, da kuma wasu da ba ‘yan Najeriya ba da suka yi rijistar yin zabe.