Rashin Lafiya A Mali Ya Samar Da Mafaka Ga 'Yan Ta'adda

Wani sojan Mali kennan, rike da takardu masu dauke da ramummukan harsashi. Junairu 21, 2013.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace rashin zaman lafiya a Mali ya samar da mafaka dake kara fadi ga ‘yan ta’adda, wadanda suke hankoron baza ikonsu.

Clinton ta gayawa wani kwamitin majalisar dattijan Amurka yau laraba cewa, Amurka da kawayenta suna aiki da makwabtan Mali wajen karfafa tsaro, musamman kasashen da basu da karfin yin haka.

Kalaman Madam Clinton sun zo ne a dai dai lokacinda sojojin Faransa da na wasu kasashen Afirka suke karuwa a Mali domin taimakawa kasar ta tusa keyar mayakan sakai masu zazzafar ra’ayin Islama da suka yi tunga a arewacin kasar.

Sakatariya Clinton, tace kawarda ‘yan tawaye daga arewacin Mali sai kasance babban kalubale.