An Cigaba Da Shari'a Akan Harin Da Aka Kawo Wa Amurka

Ana kara sauraron kararrakin harin da aka kawo wa a Amurka, ran 11 ga watan Satumbar shekarata 2001 a Guantanamo Bay.

WASHINGTON, D.C. -- A yau ne ake sauraron karraraki a zagaye na biyu kennan akan mutane guda biyar da ake zargi da kitsa hare-haren ta’addanci na ran 11 ga watan Satumbar 2001 akan Amurka.

A cikin masu kare kansu harda Khalid Sheikh Mohammed a zaman kotun da ake yi yau a sansanin sojin Amurka dake Guantanamo Bay, a kasar Cuba.

Shari’o’in da za’a cigaba da yi masu tsayi, sune zasu tabbatar idan za’a yi wa wadanda ake zargi shari’a mai adalci.

Lauyoyin wadanda ake zargi na so a yi watsi da kararrakin. Suna masu cewa jami’an gwamnatin Amurka sunyi amfani da hanyoyin da ba bisa ka’ida ba, domin uzzarawa wadanda ake zargi da amsa laifi wato, ta gana musu azaba kennan.

Lauyoyin gwamnati zasu ce hanyoyin da aka yi amfani da su domin samun wadanda ake zargi da laifi daidai ne. Sannan zasu yi kokarin gani an cigaba da rufe asirin wuraren da wadanda ake zargi suka ce an gana musu azaba, kafin a tsare su kuma a kaisu Gwantanomo.

Wasu shari’o’in da za’a gudanar a cikin wannan mako sun hada da ko za’a kira manya-manyan jami’an gwamnati su bada shaida? A ciki harda tsohon shugaban Amurka, George W. Bush.

Wadanda ake zargi dai, na fuskantar laifuffuka sama da 3,000 na kisan kai.