Wadansu 'yan kasar Rasha da Ukraine sun bayyana nasarar zaben Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a karo na shida a matsayin koma baya, yayin da kasashen yammacin duniya ke Allah wadai da zaben.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar da gagarumin rinjaye, lamarin da zai ba shi wani karin wa'adi na mulki.
Rikicin siyasa da karuwar tashe-tashen hankula a Haiti sun haifar da yanayi mai wahalar magancewa ga al'ummar Haiti.
A ci gaba da kwan gaba kwan baya da huldar Jamhuriyar Nijar da wasu kasashen Yamma ke yi, kasar da ke karkashin mulkin soji, ta yi shelar yanke huldar soji da Amurka.
Kungiyar agaji ta SOS Mediterranee a yau Alhamis ta ce, wasu da aka ceto daga wani jirgin ruwan roba da ya barke a tsakiyar tekun Mediterrenean, sun sanar da cewa, wasu mutane 50 da suka tashi daga kasar Libya tare da su mako guda da ya wuce sun halaka a cikin wannan tafiya.
Majalisar Wakilan Amurka ta zartar da muhimmin kudirin daka iya haramta amfani da manhajar Tik tok a kasar.
Kafar yada labaran kasar Rasha ta sanar a yau Alhamis cewa 'yan tawayen Houthi na Yaman sun yi ikirarin cewa suna da wani sabon makami mai linzami a ma'ajiyar makamansu.
Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta ce za su kama 'yan kasar da ke yaki da sojojin Isra'ila ko kuma tare da su a Gaza idan sun komo gida.
Shugaban kasar Vladimir Putin ya gargadi kasashen yammacin duniya a ranar Laraba cewa a shirye Rasha ta ke ta yi yaki da makamin nukiliya, yana mai cewa idan Amurka ta tura dakaru zuwa Ukraine, za'a iya daukar al'amarin a matsayin wani mummunan kazancewar rikicin
Hukumar Baitulmalin Amurka ta kakaba takunkumi ma mutane da hukumomi 16 a yankunan kuryar Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Masu aikin ceto a tekun kasar Spaniya sun ce sun ceto mutane 38 da ransu tare da samun gawarwakin wasu biyu daga cikin wani kwale-kwalen bakin haure da ya taso daga yammacin Afirka ya ke kokarin isa tsibirin Canary.
Domin Kari
No media source currently available