Ana Zargin Wasu 'Yan Tawaye Da Kitsa Juyin Mulki Akan Shugaban Congo

Lardin limpopo a Afirka ta Kudu.

Wani lauyan gabatarda karraraki na Afrika ta Kudu yayi zargin cewa wasu ‘yantawayen Janhuriyar Demokradiyyar Congo su 19, ciki harda wani dan Amurka, da laifin kitsa makiricin kifarda gwamnatin Congo din ta hanyar anfani da matakai da yawa, ciki harda musayar bada ma’adinai don a sami makamai.

A cikin bayanin da ya bada yau a birnin Pretoria, lauya Shaun Abrahams yace dukkan ‘yantawayen ‘yan wata kungiya ce da ake kira Nationalists for Renewal, wadanda babban makasudinsu shine samin horaswa da kuma makaman da zasuyi anfani da su wajen yi wa shugaban Congo Joseph Kabila juyin mulki.

Wadanda ake wa wannan zargin sun hada Ba’amurke James Kazongo wanda a can Congo aka haife shi, wanda kuma aka cafke shi tareda wasu su 18 a yayin wani samame da ‘yansandan Afirka ta Kudu suka kai shekaranjiya Talata a lardin Limpopo.

Hukumomin Afirka ta Kudu sunce har yanzu akwai sauran mutane biyu da suke nema da ake jin suna da hannu a cikin yunkurin juyin mulkin.