Najeriya Ta Sake zama Tauraruwar Kwallon Afirka

Magoya bayan Najeriya su na murnar nasarar da ta samu

A bayan fafutukar shekaru 19, Najeriya ta koma zakara a gasar cin kofin Tamaula ta kasashen Afirka bayan da ta doke Burkina Faso da ci daya mai ban haushi
Sunday Mba, shi ne zakaran wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afirka, AFCON, da aka yi a kasar Afirka ta Kudu, a bayanda ya jefa ma 'yan Super Eagles na Najeriya kwallonsu kwaya daya rak cikin ragar 'yan Burkina Faso a minti na 40 da fara wasa.

Haka aka tashi da ci daya mai ban haushi.

Rabon da 'yan Super Eagles su lashe wannan kofi tun 1994 a gasar da aka yi a kasar Tunisiya, a lokacin Stephen Keshi, kwach din Najeriya na yanzu, yana buga kwallo kuma shi ne kyaftin na 'yan wasan Najeriya.

Super Eagles Sun Zamo Zakarun Tamaula Na Afirka

Najeriya ta fara lashe wannan kofi a shekarar 1980, a zamanin gawurtattun 'yan wasanta irinsu Christian Chukwu, Emmanuel Okala, Segun "Mathematical" Odegbami, marigayi Mudashiru Lawal, Henry Nwosu da dai sauransu.

Shugaba Goodluck Jonathan da ma dukkan 'yan Najeriya su na can su na ci gaba da murnar wannan nasara da 'yan Super Eagles suka samu.