Kalaman Turkiyya Sun Bata Wa Amurka Rai

Firayim Ministan Turkiyya,Tayyip Erdogan a lokacin da yake halartar wani taron majalisar dokoki a birnin Ankara Yuni 26, 2012.

Amurka tace bata ji dadin kalaman da ta ji suna fitowa daga bakin frayim-ministan Turkiyya Recep Erdogan ba, inda yake cewa ya kamata a dauki akidar Yahudanci a matsayin wani babban laifi ne na kuntatata wa bil adaman duniya.
Jami’an Amurka sunce anas a ran Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya tado wannan maganar da kusoshin gwamnatin ta Turkiyya, kasar da zai soma ziyara a yau Jumu’a.

Jami’an sunce wadanan kalaman na “bacin rai ne” kuma masu iya bata dangatakar dake tsakanin kasashen da abin ya shafa.

A shekaran jiya Laraba ne Mr. Erdogan yake gayawa wani dandandalin Majalisar Dinkin Duniya da aka kira a birnin Vienna cewa “in dai har za’a dauki Musulunci laifi ne”, to ita ma akidar yahudanci ya kamata yi mata daukar laifi.