Amurka Zata Cigaba Da Amincewa Koriya Ta Arewa Cin Moriyar Kariya

Shugaban Koriya ta Arewa kennan, Kim Jong-un a lokacin da yake shaidar atisayen dakarun kasar.

Mataimakin Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter ya yi alkawari cewa, Amurka zata iya ci gaba da amincewa koriya ta arewa cin moriyar kariyar makaman nukiliya daga Amurka, yayinda Koriya ta Arewa take barazanar akfawa kasar da yaki gadan gadan tare da amfani da makaman nukiliya.
Bayan tattaunawa da ministan harkokin tsaron Koriya ta Kudu Kim Kwan-jin, Carter ya shaidawa manema labarai cewa, gwajin makamai masu linzami da na nukiliya da Pyongyang tayi da kuma barazanar da tayi kwanan nan ta kai hare haren makaman nukiya, ba alheri bane ga kasar dake fama da talauci da mai ido ba.

Carter yace abinda barazanar zata haifar kawai shine maida Pyongyang saniyar ware.

Jami’an tsaron Amurka sun ce Washington tana ci gaba da gudanar da ayyukan sojin na hadin guiwa da Koriya ta Kudu tare da kara yawan shingayen kare kai daga makamai masu linzami a jihar Alaska.