Chadi Ta Fara janye Sojojinta Daga Kasar Mali

Shugaba Idris Deby yace sojojin nasa sun kammala abinda ya kai su can, kuma salon yakin sari-ka-noke bdake kunno kai yanzu a Mali ba na su ba ne.
Chadi ta fara janye sojojinta daga kasar Mali, inda suka shafe wata da watanni su na taimakawa wajen yakar ‘yan kishin Islama a arewacin kasar.

Shugaba Idris Deby na Chadi yace sojojinsa sun cimma gurin aikin da ya kai su can, kuma a yanzu ba zasu iya gwabza yaki salon sari-ka-noke dake kunno kai a Mali ba.

A bayan sojojin Faransa, sojoji dubu biyu na Chadi sune mafiya yawa na wata kasar waje da suka taimakawa dakarun Mali wajen kwato yankin arewacin kasar. A makon jiya, Faransa ta janye sojoji 100 a matakin farko na shirinta na janye sojojin sannu a hankali daga Mali.

A makon jiya an kashe sojojin Chadi su uku a wani harin kunar-bakin-wake a arewacin Mali, yayin da aka kashe wasu su 13 a yaki da tsagera cikin watan Fabrairu.

Ana sa ran cewa sojojin Majalisar Dinkin Duniya wadanda yawansu zai iya kaiwa dubu 11 zasu karbi ragamar ayyukan tsaro a yayin da ake kokarin maido da kwanciyar hankali tare da gudanar da sabbin zabubbuka a kasar ta Mali.

Mali ta tsunduma cikin fitina a shekarar da ta shige a lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnati, abinda ya ba tsagera masu alaka da al-Qa’ida sukunin kwace arewacin kasar.