Faransawa Da Aka Sako Su Na Cikin Koshin lafiya

Shugaba Francoise Hollande na Faransa

An sako mutanen a bakin iyakar Najeriya da Kamaru, bayan da suka shafe kimanin watanni 2 su na hannun 'yan bindigar da aka ce na Boko Haram ne.
Faransawa bakwai da aka sako bayan da aka yi garkuwa da su na watanni biyu su na cikin koshin lafiya.

A ranar 19 ga watan Fabrairu 'yan bindiga suka sace iyalan a lokacin da suke yin hutu a arewacin Kamaru. Daga baya mutanen da suka sace su, sun yi ikirarin cewa su 'ya'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram.

Babba a cikin wannan iyali da aka sace, Tanguy Moulin-Fournier, ya fadawa 'yan jarida yau jumma'a cewa an rike su a wani wurin da ba su sani ba a bakin iyakar Najeriya da Kamaru.

Wakilin Muryar Amurka, Mamadou Danda, ya aiko da rahoto kan sakin mutanen daga arewacin Kamaru:

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoto Daga Kamaru Kan Sako Mutanen Da Aka Yi Garkuwa da Su