Ana Neman Gudunmuwar Jini a Asibitocin Abuja

Mutane a inda Bom ya fashe a tashar motar Nyanya Abuja, Najeriya.

Bayan fashewar tagwayen boma-bomai a tashar motar Nyanya dake birnin tarayyar Abuja, hukumomi sunce an rasa rayuka sama da mutum 71, da kuma sama da 100 wadanda suka jikkata. Wasu da suka rayu na bukatar tallafin jinni, shiyasa likitocin asibitocin da aka kai masu jinya suke kira ga jama'a su bada tallafin jini.
Shugaban hukumar kawo dauki na gaggawa a babban birnin tarayya Abuja, Abbas Idris yayi kira ga jama’a da su gaggauta kawo gudunmuwar jini.

Mr. Abbas yace "neman wannan taimako yazama wajibi domin bukatar da ake dashi domin yiwa wadanda suka jikkata magani."

Kawo yanzu ana samun nasarar yiwa mutane da suka ji rauni magani yadda ya kamata, kuma suna samun sauki, a cewar jami'an asibitocin.

Abbas Idris ya kara da cewa "hukumar babban birnin taraiya Abuja ta dauki nauyin dawainiyar yiwa wadanda suka ji rauni magani.

Shugaban hukumar kawo daukin gaggawa, ya jaddada cewar likitocin dake kula da wadanda suka ji rauni sunce daga dukkan alamu mutanen zasu rayu.

Your browser doesn’t support HTML5

A na Neman Jini a Asibitocin Abuja - 2'40"